Bismillahi..
YADDA AKE GYARA RUBUTU DA SAKE MASA FONTS STYLE TA WHATSAPP
```Assalamu Alaikum```
_Kamar yadda mutane da yawa suke ta tambaya, ta yaya za su yiwa rubutunsu kwalliya ta *WhatsApp* kamar yadda suke ta ganin wasu suna yi?_
*```GA AMSARKU A TAƘAICE, A SAUƘAƘE KUMA DALLA-DALLA```*
*1 YADDA AKE YIWA RUBUTU _BOLD_ (WATO YA ƊAN ƘARA ƘIBA)*
Da farko kafin ko bayan kun yi rubutunku, sai ku sanya star (*) a farko da kuma ƙarshen jimla wacce take a layi ɗaya, kamar haka:
* *Hello* *
*Abin lura:*
star (*)/tauraron ta kasance a jikin rubutun a farkon da kuma ƙarshen.
*2 YADDA AKE YIWA RUBUTU _ITALIC_ (WATO YA ƊAN KWANTA)*
Za ku sanya *Dash* (_) a farko da kuma karshen rubutu kamar haka:
_ _Haɗejia_ _
Zaku sanya shi a jikin rubutu karku rabasu. *Misali:* _Buhari _ in kun rabasu ba zasu yi ba.
*Abin lura:* _*Dash* ya ɗan sha banban da *karan ɗori (Hyphen),* saboda da shi *Dash ( _ )* ya ɗan kama ƙasa, *karan ɗori (Hyphen)* kuma ya ɗan tasa sama ( - )._
• Dash _
• Hyphen -
Banbanci: _ - _ - _ -
*3YADDA AKE YIWA RUBUTU _~STRIKETHROUGH~_ (WATO A JA MASA LAYI A TSAKIYARSA)*
Shi ma in zaku yi wannan zaku yi amafani da alamar *Tilde (~)* ne a farko da kuma ƙarshen rubutu kamar haka:
~ ~University~ ~
*4YADDA AKE MAIDA SALON RUBUTU (FONT STYLE) DAGA YADDA YAKE (ARIAL STYLE) YA KOMA ```AVANTGRADE BK BT STYLE```*
Yadda ake yin wannan zaku fara rubutun jimla ko kalma ne da alamar *` Quotation Marks (Alamar buɗe magana) wato ` ` ` guda uku a farko da kuma ƙarshen rubutu shima guda uku haɗe, kamar haka:
` `` ```Mathematics``` `` `
Sai a gwada waɗannan kafin wasu styles su ƙara fitowa.
``` ```
Alhamdulillahi..
~_*#Share*_~
No comments:
Post a Comment